Jamus: tagomashin AfD a zaben Thuringia | Labarai | DW | 28.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: tagomashin AfD a zaben Thuringia

Jam'iyyar AfD ta masu akidar kyamar baki ta samu karin tagomashi a zaben jihar Thuringia da ke gabashin Jamus da aka gudanar a karshen mako, inda ta bai wa kawancen  jam'iyyun da ke mulki na CDU da SPD tazara.  

Deutschland Landtagswahl in Thüringen - Wahlparty AfD

Jam'iyyar AfD na murnar samun karin tagomashi a Jamus

Rahotanni sun nunar da cewa jam'iyyar ta AfD ta ribanya adadin sakamakonta na shekarar 2014 har sau biyu a zaben na Thuringia, inda ta zo a matsayin ta biyu da kaso 23,5%, a yayin da ita kuma jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ta samu gagarumin koma baya a sakamakon zaben, a karon farko a jihar tun bayan sake hadewar Jamus a shekara ta 1990,  inda jam'iyyar ta sami kaso 21,8%. 

Ita ma dai jam'iyyar SPD ta ja baya a zaben, inda ta samu kaso takwas da digo biyu (8,2%) cikin dari, a yayin da ita kuwa jam'iyyar Green da FDP suka samu kaso fiye da biyar cikin dari na kuri'un da aka kada.

Jam'iyyar Die Linke ce dai ta Firaminista Bodo Ramelow ke zama jagorar jam'iyyu a zaben na Thuringia da ke gabashin Jamus, inda ta sami sama da kaso 30 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben.