Jamus ta Gabas yanki ne na Jamus da aka girka shi a shekarar 1949. Yankin dai na bin tsari ne na kwamunisanci a wancan lokacin.
A cikin shekara ta 1990 Jamus ta Gabas ta hade da Jamus ta Yamma bayan faduwar katangar Berlin. Wannan hadewar da yankunan biyu suka yi ne ya haifar da Tarayyar Jamus.