Sudan ta Kudu ta samu 'yanci daga Sudan a watan Yuli na shekara ta 2011 bayan yakin basasa na tsawon lokaci.
Mutanen Sudan ta Kudu sun tayar da kayar baya sakamakon wariya da suke gani Larabawa na arewacin Sudan suna nuna wa bakaken fata na yankin kudanci. Haka ya janyo yakin basasa amma yarjejeniyar zaman lafiya ta taimaka Sudan ta Kudu ta balle daga cikin Sudan.