1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashe-kashen kabilanci a Sudan ta Kudu

Mouhamadou Awal Balarabe
June 9, 2023

Akalla mutane 13 sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a wani rikicin kabilanci da ya barke a cibiyar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don kare fararen hula a Sudan ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4SPK0
'Yan gudun hijira na yawaita a Sudan da kasar Sudan ta KuduHoto: JOK SOLOMUN/REUTERS

Sanarwar da hukumar bada agaji ta OCHA ta fitar ta nunar da cewa, mutuwar wani matashi dan kabilar Shilluk bayan da aka daba masa wuka ne ya kunna wutar rikicin a sansanin Malakal da ke tazarar kilomita 520 daga arewacin babban birnin kasar Sudan ta Kudu wato Juba. Wannan yanayi na rashin tsaro ya kawo cikas ga ayyukan jin kai, tare da haddasa dakatar da aikin jigilar 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu da ke tserewa rikicin Sudan.

Duk ma da kasancewarta 'yar auta a cikin kasashen duniya, amma Sudan ta Kudu na fama da rikice-rikicen siyasa da kabilanci da rashin zaman lafiya tun bayan samun ‘yancin kai daga Sudan a shekarar 2011. Ko da kafa gwamnatin rikon kwarya da aka yi bayan yakin basasa, bai hana tashe-tashen hankula ya ci gaba da zubar da jini a Sudan ta Kudu mai arzikin man fetur ba.