Yakin Duniya na Biyu ya barke a shekarar 1939 bayan mamaya da sojojin Jamus karkashin gwamnatin Adolf Hitler ta 'yan Nazi suka yi wa kasar Poland.
Yakin ya kawo karshe a shekarar 1945 lokacin da sojojin kawance na yamma da kuma na Soviet suka mamaye birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Sannan sojojin Japan a yankin Asiya suka mika wuya ga sojojin Amirka.