Bikin cika shekaru 77 da Rasha ta yi nasara a yakin duniya na biyu | BATUTUWA | DW | 09.05.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Bikin cika shekaru 77 da Rasha ta yi nasara a yakin duniya na biyu

Rasha na bikin cika shekaru 77 da nasara kan 'yan Nazin Jamus a lokacin yakin duniya na biyu, a daidai lokacin da take ci gaba da mamayar makwabciyarta Ukraine.

A jawabinsa na bikin cika shekaru 77 da yin nasara a yakin duniya na biyu, Shugaba Putin ya tabbatar wa dubban al'ummar kasar da suka halarci bikin cewar sojojin Rasha da ke fagen daga a Ukraine na yaki ne domin kare martabar kasarsu da ma makomarta a nan gaba, inda ya ce "Kwazo da kuma turjiya ta dan kasa nagari, sojojinmu suna yaki da maikiyanmu a kusa da biranen Moscow da Leningrad da Kyiv da Minsk, kuma a wannan kwanakin sun ci gaba da yaki domin 'yan uwanmu da ke Donbass, da kare martabar tsaron kasarmu."

Dakarun Rasha sama da dubu goma sha daya ne suka halarci wani faretin soja da aka gudanar a yayin bikin,  kana wani abu da ke kama da nuna karfin sojinta, Rasha ta baje kolin manya da kananan tankokin yaki a dandalin Red Square da ke fadar mulki ta Kremlin.

Karin Bayani : Rikicin Rasha da Ukraine na ci gaba da shafar duniya

Shugaba Volodmyr Zelensky  na ci gaba da musanta hujjojin Putin na kai farmaki a Ukraine saboda 'yan Nazi. A jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo Zelensky ya ce Rasha ya kamata ta manta da nasara kan 'yan Nazi don duk abin da suka yi a wancan lokacin shi ne Rashar ke yi a yanzu inda ya ce "Muna farin cikin zagayowar ranar da kasarmu da sauran kasashe suka yi nasara a kan 'yan Nazi kuma ba za mu bar wata kasa ta karbe mana wannan nasara ba".

Karin Bayani : Turkiyya za ta sasanta shugabannin Rasha da Ukraine

Kasashen duniya da ke Allah wadarai da mamayar Rasha a Ukraine sun yi fargabar Shugaba Putin ya ayyana yakin na Ukraine a hukumance, matakin da iya tunzura NATO da Kungiyar Tarayar Turai da Amirka daukar wasu matakai.    

A bin jira a gani a yanzu shi ne matakin da kungiyar taro ta NATO da Kungiyar Tarayyar Turai da Amirka za su dauka kasancewar Rasha ta kauce ayyana mamayar da take yi wa Ukraine da sunan yaki a hukumance kamar yadda a kayi fargaba daga farko.

Sauti da bidiyo akan labarin