1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ukraine da Rasha a taron NATO

Abdoulaye Mamane Amadou
March 4, 2022

Ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO za su gudanar da taro a wannan Juma'a domin tattaunawa kan mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/47zCG
Brüssel Belgien | NATO Sitzung zur Ukrainekrise - Jens Stoltenberg
Hoto: Olivier Matthys/AP/picture alliance

Sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken zai halarci taron tare da sakataren kungiyar NATO Jens Stoltenberg da kuma ministan harkokin wajen Ukraine Dimitro Kuleba. Sauran wadanda aka gayyata sun hada da Ministar harkokin wajen Birtaniya Liz Truss da ta Canada Mélanie Joly.

Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken zai kuma kai ziyara gabashin Turai domin tattaunawa da wasu aminan kasashe game da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine. A gobe Asabar zai isa kasar Poland kafin ya wuce zuwa Moldova da Lithuania da Latvia da kuma Eastonia. Ziyarar na zuwa ne yayin da aka shiga kwana tara na mummunan farmakin da Rasha ke kaiwa a Ukraine.