Shiri ne da sassa shidda na nahiyar Afirka na DW ke gabatarwa kan irin sauyin da mutane ke taimakawa wajen samarwa a Afirka.
AoM shiri ne da aka yi wa lakabi da ''Sauyi a Afirka'' wanda ke duba irin yadda mutane a nahiyar Afirka ke amfani da hanyoyi daban-daban wajen kawo sauyi. Shirin ya kunshi rahotanni na bidiyo da na rediyo da kuma irin rahotannin da ake wallafawa a shafin intanet na gidan rediyon DW.