Kungiyar Kasashen Larabawa ta Arab League ta kunshi kasashen Larabawa da ke arewacin Afirka da kuma wanda ke yankin Gabas ta Takiya.
An kafa kungiyar ta Arab League a shekara ta 1945 kuma ta na da kasashe 22 da ke zaman mambobi. Makasudin kafa kungiyar shi ne kyautata dangantaka tsakanin kasashen Larabawa.