1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Siriya. Dubbai sun bace sakamakon yaki

Mahmud Yaya Azare LMJ
February 21, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta kirkiri hukumar neman 'yan Siriya kimanin dubu 130, wadanda suka bata lokacin yaki.

https://p.dw.com/p/4ciS9
Siriya | Yaki | Gudun Hijira | Bacewa
Miliyoyin al'ummar Siriya na gudun hijira a kasashe da damaHoto: Omar Albam/DW

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kirkiri wannan hukuma mai zaman kanta, domin fayyace makomar dubban 'yan kasar ta Siriya da ba a san inda suka shiga ba tun bayan barkewar yaki a kasar a shekara ta 2011. Matakin na Majalisar Dinkin Duniya dai, ya biyo bayan damuwar da aka nuna a Damascus kan wadannan dubban mutane. Majalisar Dinkin Duniyar ta nunar da cewa, bayan kwashe shekaru 12 na rikici da yaki a Siriyan za a iya cewa ba a samu nasara sosai ba wajen kawar da radadin da iyalai ke ciki na samar da amsoshi kan makoma ko labarin dukkan mutanen da suka bata. Sai dai kum a hannun guda, mahukuntan kasar na nuna damuwarsu kan wannan hukuma da kasashe 83 suka kada kuri'ar amincewa da ita. Koda yake wasu kasashen 11 sun hau kujerar naki ciki har da Siriyan da Chaina da Iran da Rasha, yayin da kasashe 62 kuma suka kauracewa zaman tattaunawa kan kudurin.