Guguwar neman sauyi ta kada a kasashe da dama na Larabawa inda mutane suka bukaci sauyin shugabanci.
Wannan guguwa ta da faro daga shekara ta 2010 ta fara yin awon gaba da gwamnatin Tunisiya daga bisani ta bulla a kasashen da suka hada da Masar da Libiya da Siriya da Bahrain da Saudiyya.