1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afrika a jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar M. Ahiwa
March 22, 2024

Kokarin halasta kaciyar mata a Gambiya da sake dawo da hukuncin kisa a Kwango da samar da dala biyan bakwai da Tarayyar Turai ta bai wa Masar, sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4e2N2

Za mu fara da jaridar die Tageszeitung wadda ta wallafa labari mai taken "Gambiya ta kama hanyar dawo da al'adar yi wa yara mata kaciya, al'adar da duniya ta yi watsi da ita".

Gambiyar dai na iya zama kasa ta farko da ta dage haramcin yi wa mata kaciya. Tun daga farkon watan Maris ne aka fara tattaunawa kan wani kudirin doka da wani dan majalisa Almammeh Gibba ya gabatar wanda zai sake ba da damar yin hakan.

Hujjoji da ya gabatar dai sun hada da tsarkake addini da kare ka'idoji da dabi'u da kuma mutunta al'adu. Tuni ma dai wannan kudurin doka ya shige karatu na biyu tun a farkon wannan makon.

'Yan majalisar wakilai 42 daga cikin 49 da suka hallara, sun kada kuri'ar amincewa da wani kwamitin da aka dora wa wannan alhaki, da ya kara yin nazari kan kudirin dokar da ke cike da cece-kuce.

Shekaru goma ke nan da dage wannan doka a kasar ta Gambiya, inda shirin sake maido da shi ke fuskantar fushin wasu rukunai na al'ummonin kasar da suka hada da kungiyoyin kare hakkin mata da na dan Adam. Duk da cewar ba a san lokacin da za a kai ga amincewa da zartar da wannan doka ba, matakin da ake ciki a yanzu haka ya janyo zanga-zanga musamman a bangaren matan da kungiyoyin kare hakkin dan Adam.

Tsohuwa mai yi wa mata kaciya
Tsohuwa mai yi wa mata kaciyaHoto: Sally Hayden/Sopa Images/Zuma Press/Imago

"Ministan shari'a na son yin amfani da hukuncin kisa don ceton Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango daga masu cin amanar kasa" Sai dai akwai babban gibi tsakanin dokar a zahiri da kuma yiwuwar aiwatar da ita a wannan kasa ta yankin gabashin Afirka a cewar jaridar Der Tagesspiegel a cikin labarin da ta wallafa kan wannan kasa da ke fama da rigingimun kungiyoyin tawaye.

Jaridar ta ce akwai sabanin haka dangane da hukuncin kisa,  domin duk da cewar akwai tanadin hakan a cikin doka tsawon shekaru kena ba a aiwatar da shi ba a zahiri. Amma wannan na iya canzawa yanzu. A wata takardar da ta aike wa hukumomin shari'a mai dauke da kwanan watan 13 ga Maris, ministar shari'a Rose Mukombo ta sanar da janye dakatar da aiwatar da hukuncin kisa da aka yi tun shekara ta 2003.

Ta ce hakan zai taimaka wajen tsarkake sojojin kasarmu daga maciya amana da kuma dakile bullar ta'addanci da 'yan fashi da makami. Majalisar ministocin ta zartar da wannan batu a ranar 9 ga Fabrairu, in ji ta. "A lokacin yaki, a karkashin dokar soji ko dokar ta-baci, a zaman wani bangare na aikin 'yan sanda don kiyayewa ko maido da zaman lafiyar jama'a ko kuma a cikin wani yanayi na musamman", ana iya aiwatar da hukuncin kisa ga mutane da aka samu da manyan laifuka daban-daban kamar kisan kare dangi da makamantansu.

Bari mu karkare shirin da sharhin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa a kan shirin Tarayyar Turai na biyan samar da Euro biliyan 7 a matsayin sakayya ga Abdelfatah al-Sisi. Ana saran shugaban na Masar zai taimaka wajen hana bakin haure shiga Tarayyar Turai.

Kungiyar Tarayyar Turai ta kulla sabuwar yarjejeniya a kan bakin haure. A wannan karon tare da Masar, kasa mafi yawan al'umma a yankin kasashen Larabawa. Don haka, shugabar hukumar EU Ursula von der Leyen ta tashi zuwa Masar a ranar Lahadi tare da rakiyar shugabannin gwamnatocin Italiya da Girka da Austria da Belgium da Cyprus.

Wannan yarjejeniya dai a cewar manazarta ba komai ba ce fa ce, katse kwale-kwalen 'yan gudun hijira da rufe kan iyakar Libiya. Kasancewar a zahiri 'yan ci-rani kalilan ne ke tashi daga gabar tekun Masar zuwa Turai. Don haka yarjejeniyar da Masar ta dace da jerin yarjejeniyoyin makamanciyarta da kungiyar EU ta rattabawa hannu da kasashen da ke kewayenta kamar Tunisiya da Moritaniya.