Masar kasa ce da ke kan gaba wajen yawan al’umma a cikin jerin kasashen Larabawa.
A cikin shekarar 2011 ne kasar ta fuskanci boren al'umma da ke adawa da mulkin Hosni Mubarak daidai lokacin da guguwar neman sauyi ta kada a kasashen Larabawa. Masar kasa ce da ke da karfin fada a ji a yankin gabas ta tsakiya.