Wata kotun kungiyar tarrayar Turai ta yi watsi da karan da tsohon shugaban kasar Masar Hosni Mubarak ya daukaka na rike wasu kudadensa da ake ci gaba da yi a cikin bankuna cikin wasu kasashe na EU.
Kotun ta kungiyar EU da ke a Luxemburg ta kori karan sannan ta kara tsawaita ci gaba da rike kudaden na tsohon shugaban kasar Masar din a cikin bankuna. Hosni Mubarak mai shekaru 90 da haifuwa a shekara ta 2011 wata kotun a Masar ta wankeshi a game da zargin da ake yi masa na kisan masu zanga-zanga, sai dai kuma an ci gaba da tsareshi a gidan kurkuku a kan laifin cin hanci, tun a shekara ta 2011 bayan juyin juya halin da ya shareshi daga mulki.