Yakin an fafata mafi yawasa kasashen Turai, amma ya zama na farko da ya kunshi galibin kasashen duniya, saboda lokacin Turawa suna mulkin mallaka.
Yakin ya barke a shekarar 1914 bayan kisan yarima Archduke Franz Ferdinand na Ostiriya a birnin Sarajevo na Bosniya. Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen Turai na taimakawa ko kare juna daga wata barazana ta taimaka wajen barkewar yakin.