1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukin ranar yara ta duniya a Jamus

September 20, 2006
https://p.dw.com/p/Buin

A bukin ranar yara ta duniya da ake gudanarwa yau a fadin tarayyar Jamus, kungiyar kyautatawa yara ta Jamus ta rarraba tutoci masu launin shudi har guda miliyan 2 da rabi. Kungiyar ta ce dalilin yin haka dai shine yara kimanin miliyan biyu da rabi ke rayuwa cikin matsanancin talauci a fadin Jamus. Wadanda suka shirya bukin na yau a manyan biranen kasar sun ce yawan kananan yara dake fama da talauci a Jamus ya ninka sau biyu tun bayan shekara ta 2004. SGJ Angela Merkel ta nuna goyon baya ga kyautata ilmin kananan yara a cikin kasar. Ta ce tun gabanin yaro ya cika shekarun shiga firamare ake fara ilmantar da shi.