Cikas a kafa rundunar yaki da Boko Haram | Siyasa | DW | 20.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Cikas a kafa rundunar yaki da Boko Haram

Rashin yarda da juna tsakanin kasashen Najeriya da Kamaru da ke makwabtaka da juna kan yadda za a tura sojoji domin su yaki Boko Haram ya kawo nakasu wajen kaddamar da rundunar sojojin.

Rundunar sojojin da za ta yaki kungiyar masu tsattsauran ra'ayin ta Boko Haram dai za ta kunshi dakaru daga kasashen da ke makwabtaka da Najeriyar da suma Boko Haram din ke zama barazana a garesu. Gaza kaddamar da rundunar sojojin hadin gwiwar da za ta kunshi kimanin dakaru 2,800 kamar yadda aka tsara a watan Nuwambar shekarar da ta gabata ta 2014, ya sanya masu ta da kayar bayan sun kwace garuruwa masu yawa a yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriyar. Kwace sansanin rundunar sojoji a Baga da ake tsammanin za ta zamo shalkwatar sojojin hadin gwiwar da kuma kashe akallah mutanen garin 2,000, ya nuna karara illar da ke tattare da rashin samun hadin kai tsakanin Najeriyar da Kamaru.

Rashin hadin kai tsakanin Najeriya da Kamaru

A cewar wani mai fashin baki a cibiyar bayar da shawarwari a kan al'amuran da suka shafi nahiyar Afirka da ke London Imad Mesdoua matsalar da ke hana samar da rundunar sojojin hadin gwiwar ta kasashen da ke makwabtaka da Najeriya, ta samo asali ne tun daga rashin yadda da juna da ke tsakanin kasashe biyu da suka fi kowa ruwa da tsaki a rikicin na Boko Haram wato Najeriya da Kamaru. A Talatar nan ne aka bude wani zaman taro a Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar a kan batun yaki da kungiyar ta Boko Haram, wanda ya samu halartar kasashe 13 na Afirka da kuma wasu kasashe da ba na Afirka ba. Kasashen Jamus da Kanada da China da Spain da Amirka da Faransa da kuma Ingila. Ministocin harkokin kasashen waje na Benin da Kamaru da Equatorial Guinea da Chadi da kuma Nijar.

Hada karfi da kungiyoyin kasa da kasa

An kuma samu halartar manyan kungiyoyin kasa da kasa, kamar su CBLT ta kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da kungiyar CEN-SAD ta kasashen yankin Sahel da kungiyar Tarayyar Afirka AU da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar kasashe Musulmi ta OIC. Da ya ke magana yayin bude taron, ministan harkokin wajen kasar Nijar Mohamed Bazoum, ya ce sanin kowa ne yanayin tsaro a Tarayyar Najeriya da kuma yankin tafkin Chadi ya yi mummunar tabarbarewa musamman ma dangane da kama garin Baga da ke da matukar muhimmanci a farkon wannan wata na Janairu da kuma yadda 'yan kungiyar Boko Haram din ke amfani da manyan makamai.

Sauti da bidiyo akan labarin