Nkosozana Dlamini-Zuma na daga ciin wanda suka jima suna fafutuka wajen ganin an kawar da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. An haife ta a shekarar 1949.
Ms Dlaminin-Zuma wadda tsohuwar mai dakin Jacob Zuma ce ta rike mukami na minista a ma'aikatu da dama a Afirka ta Kudu kafin daga bisani a zabeta a matsayin shugabar kungiyar kasashen Afirka ta AU a shekara ta 2012.