Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Kungiyar tarayyar Afirka ta AU ta gudanar da babban taronta inda ta zabi sabon shugaba mai suna Faki Mahamat don maye gurbin Nkosozana Dlamini-Zuma wadda wa'adin mulkinta ya zo karshe.
Ministan harkokin wajen na Chadi ya doke sauran 'yan takara hudu na kasashen Kenya da Botswana da Equatorial Guinea da Senegal, domin shugabantar kungiyar ta Tarayyar Afirka. (30.01.2017)
An bude taron kungiyar Tarrayar Afirka wato AU karo na 28 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha wato Ethiopia, inda za a tattauna batun sake mayar da kasar Maroko cikin AU da zabar wanda zai gaji Nkosazana Dlamini Zuma. (30.01.2017)
Taron shugabannin kasashen Afirka da ya gudana a birnin Addis Ababa na Habasha ya dauki matakan da suka hada da sake mayar da Mokoro cikin kungiyar da gami da zaben sabon shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar. (31.01.2017)
Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU, ya taya murna ga zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na lashe babban zaben kasar da ya gabata.
Hankalin jaridun na Jamus a wannan makon ya karkata zuwa kan babban zaben Najeriya da taron AU da kuma kudirin Jamus na daukar kwararru a Ghana.
Kungiyar AU ta yi kira da a kaddamar da bincike tare da tunasar da kasashe kan mutunta 'yan ci-rani kamar yadda dokoki suka yi tanadin hana amfani da karfi a kan 'yan ci-ranin.