1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faki Mahamat ya zama sabon shugaban AU

Zainab Mohammed Abubakar
January 30, 2017

Ministan harkokin wajen na Chadi ya doke sauran 'yan takara hudu na kasashen Kenya da Botswana da Equatorial Guinea da Senegal, domin shugabantar kungiyar ta Tarayyar Afirka.

https://p.dw.com/p/2WgHJ
Äthiopien Debatte der Präsidentschaftskandidaten der Kommission der Afrikanischen Union
Hoto: DW/C. Wanjohi

Faki ya doke sauran 'yan takara hudu domin haye kujerar Nkosazana Dlamini-Zuma, ta kasar Afirka ta Kudu, da wa'adinta ke karewa.

Tsohon shugaban kasar Burundi Pierre Buyoya ya tabbatarwa manema labaru nasarar Faki, bayan zagayen karshe na fafatawa da ministar harkokin wajen Kenya Amina Mohammed.

Mai shekaru 56 kuma tsohon fraiminista dai, Faki ya kasance a gaba wajen yakar masu tsattsauran ra'ayi na Najeriya da Mali da Sahel, kuma tuni ya yi alkawarin cewar, samar da ingantaccen tsaro shi ne na farko a agendarsa a matsayin shugaban hukumar mai wakiltar nahiyar mai dumbin al'umma.

Baya ga Kenya, sauran kasashe da suka yi takara sun hadar da Botswana da Equatorial Guinea da Senegal.