Chadi tana cikin kasashen yankin tsakiyar Afirka wadda Faransa ta yi wa mulkin mallaka kafin samun 'yanci a shekarar 1960.
Duk sauyin gwamnatin da aka samu a kasar yana zuwa ta hanyar tashe-tashen hankula gami da tawaye. Kasar ta yi makwabtaka da kasashen da suka hada da Najeriya, da Kamaru, da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da Jamhuriyar Nijar, da Libiya da kuma Sudan.