Rasha ta ce Chadi ta kama 'yan kasarta uku ba dalili
September 24, 2024Rasha ta tabbatar da cewa gwamnatin Chadi ta kama 'yan kasarta uku da kuma wani 'dan kasar Belarus guda daya, ba tare bayyana wani dalilin kamen na su ba.
Karin bayani:Chadi: Cin hanci da karbar rashawa na karuwa a mulkin Deby
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayyana sunayen 'yan kasarta da aka kama da Maxim Shugaley da Samer Sueifan, da kuma E. Tsaryov, da kuma 'dan Belarus mai suna A. Denisevich, to amma ta yi nisa wajen tattaunawa da gwamnatin Chadi domin sakin mutanen.
Karin bayani:Ministan harkokin wajen Rasha na ziyara a Afirka
Daya daga cikin wadanda kama mai suna Maxim Shugaley, na daga cikin mutanen da EU ta kakaba wa takunkumi, kasancewarsa guda cikin jigajigan jami'an da suka yi aiki da kamfanin tsaro na Wagner, karkashin jagorancin Yevgeny Prigozhin.