Kamaru tana cikin kasashen yankin tsakiyar Afirka wadda Faransa ta yi wa mulkin mallaka zuwa shekarar 1960.
A shekarar 1961 aka hade yankunan kasar masu magana da harshen Faransanci da masu magana da harshen Ingilishi. Kuma kasar ta dauki harsunan na Faransanci da Ingilishi a matsayin harsuna da ake amfani da su a hukumance.