1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiJamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin tasku

November 28, 2024

Yajin aikin da direbobin manyan motocin dakon kaya suka shiga a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ya haifar da hauhawar farashin kayan masarufi a kasar har ma da makwabciyarta Kamaru.

https://p.dw.com/p/4nXTu
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Shugaban Kasa | Faustin-Archange Touadera | Kunci
Shugaba Faustin-Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: DW/J. M. Bares

Gamayyar kungiyar direbobin manyan motocin dakon kayan da galibinsu 'yan kasar Kamaru ne, ta tsunduma yajin aikin a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a nufin nuna fushi kan zargin sojojin hayar Rasha na Wagner da halaka guda daga cikin mambobinsu. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar dai na zaman guda cikin kasashe matalauta a duniya, kuma ta dogara ne da kasashe makwabta wajen samun kayan bukatun yau da kullum musamman daga makwabciyar kasaKamaru. Wani rahoto da Cibiyar Kasuwanci ta Duniya ta fitar a shekara ta 2022 ya nunar da cewa, kaso 40 cikin 100 na kayan bukatun yau da kullum a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, na fitowa ne daga Kamaru.

Karin Bayani: Taron Hukumar Hana Fasa Kwabri ta Afirka

To amma duk da huldar kasuwancin da ke tsakanin Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, 'yan kasuwar kasar ta Kamaru sun sha alwashin daina shigar da kaya Bangui har sai an bi musu hakkinsu na halaka direban da ake zargin sojojin hayan Rasha na Wagner sun yi da ake yawan samun tsamin dangantaka da rashin fahimtar juna tsakaninsu da al'ummar yankin tun lokacin da suka yi kaka-gida a 2018. Kisan direban ya kara ta'azzara halin da ake ciki na kuncin rayuwa da kangin talauci da al'umma ke ciki. Wani mazaunin Bangui da ke sana'ar gyaran wayar hannu Grace-a-Dieu Ndomoyando ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, wannan lamari ya sake mayar da hannun agogo baya a kokarinsu na neman abin rufawa kai asiri.

Tserewa daga rikicin Afirka ta Tsakiya

Shi kuwa wani dan kasuwan Bangui Magloire Guerematchi ya shaida wa AFP din cewa, tun lokacin da direbobin Kamaru suka shiga yakin aikin komai ya tsaya cak a daukacin kasuwannin da ke fadin kasar. Kamaru dai ta yi iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta mashigin jiragen ruwa da ke birnin Douala a gabar tekun Atlantika, to amma dai babbar ayar tambayar ita ce yanayin zaman zullumi da ake ciki a birane kamar Garoua- Boulai da ke nisan mil 725 da Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar. Mai magana da yawun direbobin motocin dakon kayan Hamadou Djika ya shaida wa AFP cewa, sun dau damarar ci gaba da zaman dirshan har sai an bi musu hakkinsu kan kisan mambansu da sojojin Wagner suka yi.

Karin Bayani: Touadera na son inganta alaka da Faransa

To ko me direbTouadera na son inganta alaka da Faransaobin kananan motocin Bangui ke cewa? Jean-Finel Danoui guda ne daga cikinsu, ya kuma nuna takaicinsa kan matakin da takwarorinsu suka dauka. A wani taron manema labarai da ta kira Ministar harkokin wajen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Sylvie Baipo-Temon ta ce shirye-shirye sun yi nisa wajen warware takaddamar da ke tsakaninsu ta fuskar diflomasiyya, duk da cewa ta ki amsa laifin sojojin hayan Rasha na Wagner din kan kisan direban babbar motar. Tuni dai kasashen Yammacin Duniya ke ci gaba da tir kan ayyukan sojojin hayar na Wagner wajen wuce makadi da rawa. Bangui dai na cikin wadi na tsaka mai wuya tun lokacin da kawancen sojojin sa-kai suka hambarar da gwamnatin Francois Bozize a 2013, wanda hakan ya bai wa Faransa tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya damar shirya zabe a kasar a 2016 da ya bai wa shugaba Faustin-Archange Touadera nasara.