Yamai shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijar. Ya na daya daga cikin biranen kasar da ke da yawan jama'a musamman 'yan kasashen waje.
Fadar gwamantin Nijar da majalisar dokoki da kuma manyan ma'aikatun gwamnati da ofisoshin jakadaci da ke Nijar duka su na birnin na Yamai.