1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kammala janye sojojin Jamus a Yamai

July 10, 2024

Jamus ta ce za ta kammala rufe sansanin sojan samanta da ke birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, a ranar 31 ga watan Augustan wannan shekara ta 2024.

https://p.dw.com/p/4i7Sw
Mali | Sojoji | Jamus
A baya dai Mali ta tilasta Jamus din ta janye sojojinta daga kasartaHoto: DW/U. Bauer

Rundunar sojan Jamus ta cimma yarjejeniyar wucin-gadi da mahukuntan Nijar ne kan tsawaita zaman dakarunta har zuwa karshen watan Mayun da ya gabata, bayan dakarun MINUSMA da Jamus din take ciki ta kammala fita daga Mali bisa rashin fahimtar juna daga bangarorin biyu.  Duk da amincewar da Nijar da Jamus din suka yi da farko, daga karshe rashin fahimtar juna ya kunno kai dangane dan wasu muhimman batutuwa ciki har da rashin tabbas game da batun bai wa sojan Jamus da ke jibge a Nijar kariya. Majalisar mulkin sojan Nijar din ta CNSP ta sanar da cewa ba za ta ba su kariya ba, lamarin da ya tilasta gwamnatin Berlin daukar matakin kwashe sojojinta da ke da sansani a birnin Yamai a karshen watan gobe. Batun na rashin bai wa sojojinsu kariyar dai ya kara harzuka mahukuntan Jamus din matuka, a cewar dan majalisar dokoki Christian Schmidt da ke kuma zaman mamba a kwamitin tsaro na majalisar dokokin Jamus ta Bundestag kana mamba a kwamitin tuntubar juna na kasashen biyu.

Nijar | Sojoji | Jamus
Sojojin Jamus na shirin kammala bankwana da NijarHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Sai dai kuma duk da ficewar dakarun sojan na Jamus daga Nijar har yanzu ba a yanke kauna ba a cewar dan majalisar, domin kuwa bangarorin biyu ka iya ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu. Ko da yake dan majaisar dokokin ta Bundestag Schmidt ya ce, dakarun sojan Jamus ka iya duba hanyoyin da ya dace su mika wa takwaransu na Nijar kayan aikin da ba su da wata bukatar kwashewa nan take. A cikin yanayi na shagube Schmidt ya kara da cewa, sojojin na Jamhuriyar Nijar ka iya amfana da kayan har ma sababbin abokan huldarsu na Rasha su ci gajiya. Dangane da batun inda kasar Jamus din za ta karkata akala kuwa domin jibge dakarunta da zarar ta fice daga Nijar, a cikin wani yanayi na rashin tabbas Schmidt ya nunar da cewa za su sake nazarin sharudan da aka gindaya mana kuma za su duba hanyoyin inganta duk wata hulda da za su yi a tsakaninsu tun daga tushe da hukumomin da ke kan karagar mulki. Dan majalisar dokokin na Jamus Christian Schmidt ya ce kawancen Sahel Alliance da ministar harkokin raya kasa ta gwamnatin Jamus Svenja Schulze ke jagoranta mai mazauni a birnin Nouakchott na kasar Murtaniya, ka iya taimakon Jamus wajen bibiyar al'amurra a yankin.