Boko Haram kungiya ce da ta yi suna wajen kai hare-hare na ta'addanci a Najeriya da kasashen da ke makotaka da ita.
Kungiyar ta Boko Haram da ke da kaifin kishin addini ta fi maida hankali ne wajen kai farmaki a arewa maso gabashin Najeriya musamman ma jihar Borno. Tada kayar bayan kungiyar ya yi kamari tun bayan kashe shugabanta Mohammed Yusuf da aka yi. A baya shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya ayyana inda suka kame a matsayin daular Islama bayan da ya yi mubayi'a ga kungiyar IS.