A Najeriya rahotanni da ke cin karo da juna na cewa jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya ji rauni, a yayin wani gumurzu tsakanin magoya bayansa da na kungiyar ISWAP.
Wata majiyar sirri ta shedawa kamfanin dillancin labarai na AFP da cewar, a wannan Larabar ce mayakan kungiyar ISWAP suka fafata da 'yan kungiyar Boko Haram karkashin jagorancin Abubakar Shekau a dajin Sambisa, inda a wani yunkuri na kin bayar da kai, Shekau din ya kudiri anniyar kashe kansa, da bindiga tare da raunata kansa.
Ko da yake ya zuwa yanzu ana samun labarai masu karo da juna kan batun raunin jagoran na kungiyar ta Boko Haram, wasu majiyoyi na cewar ya harbi kansa ne da kansa a kirgi, a yayin da wasu kuma ke nuni da cewar ya tayar da wani abin fashewa da ke daure a jikinsa don kin mika wuya ga mayakan kungiyar ISWAP.