1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Abubakar Shekau ya mutu a cewar ISWAP

June 7, 2021

Kungiyar Boko Haram mai alaka da ISIS ta sanar da hallaka Abubakar Shekau jagoran 'yan Boko Haram a cikin wani sako da ta fitar, masana dai na cewa rashin Shekau ba zai kawo karshen ta’addanci ba.

https://p.dw.com/p/3uXt0
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

A sakon muryar da ya fitar shugaban kungiyar ISWAP mai ikrarin jihadi a yankin yammacin Afirka da ke da alaka da ISIS Abu Musab al-Barnawi ya tabbatar a wani bayani cikin harshe Kanuri yana cewa Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram ya hallaka kansa, bayan da su ka rutsa sa ya rasa mafita. Abu Musab al-Barnawi da ne ga shugaban farko da ya assasa kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf wanda ya jagorancin ballewa daga jikin Abubakar Shekau saboda sabanin akida da kuma sabawa manufofin uwar Kungiyar ISIS. A ci gaban jawabin shugaban kungiyar ya bayyana dalilai na daukar matakin hallaka Abubakar Shekau bisa umurni daga babban Khalifan su, da kuma hakan ya kawo karshen rade-radin da ake yi na mutuwar Abubakar Shekau ganin an shafe tsawon lokaci bangaren sa bai fito ya musanta mutuwar ba sabanin yadda aka saba yi a baya.

Karin Bayani: Tserewa saboda fargabar hare-hare

Masu bibiyar lamarin na ganin ba mamaki jama’a za su yi murna da mutuwar Abubakar Shekau duk da cewa hakan ba zai kawo karshen zubar da jini da ake yi a wannan yankin ba kamar yadda aka saba. Kana wasu na cewa mutuwar Abubakar Shekau za ta bude sabon shafi na kalubalan tsaro ga kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da yanzu haka ke fama da hare-haren bangarorin kungiyar Boko Haram saboda yadda mai alaka da ISIS wato kungiyar ISWAP za ta hade da sauran kungiyoyin da ta ke alaka da su a sassan nahiyar Afirka.

Karin Bayani:  Tabarbarewar tsaro a Najeriya

Wasu daga dalilan kungiyar ISWAP na kashe Shekau akwai cewaakwai cewa yana cin zarafin jama'a akwai cewa yana cin zarafin jama'a da kashe fararen hulla da kwace kayayyakin jama'a, lamarin da ya sabawa manufofin kungiyar mai alaka da ISIS. Ko da yake akwai masu hasashen cewa wadannan hujjojin basa rasa nasaba da sabon salo na samun hadinkai da tunanin talakawa a ikrarin da suke na yada da'awar jihadi a yankunan Najeriya. Har yanzu gwamnati a tarayyar Najeriya da ma rundunar tsaron kasar da ke yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda ba su ce komai kan sabon labarin mutuwar Abubakar Shekau din ba, inda masana ke cewa kallo ya koma sama ana jiran martanin bangaren Boko Haram da kuma fitowar manufofin kungiyar ISWAP domin a san inda ta dosa.