Tafkin Chadi tafki ne da ke da muhimmancin gaske ta fuskar tarihi da kuma tattalin arziki musamman ga ksashen da ke kewaye da shi.
Tafkin na samar da ruwa ga mutane kimanin miliyan 68 da ke Niger da Najeriya da Kamaru da kuma Chadi. Matsaloli da ke da nasaba da muhalli sun sanya tafkin janye wa da kusan kashi 95 cikin 100 amma a wasu hotuna na tauraron dan Adam da aka dauka a shekarar 2007 sun nuna cewar tafkin ya fara farfadowa daga kafewar da ya yi.