1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta sace makiyaya 30 a Nejeriya

June 7, 2023

Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sace makiyaya akalla 30 a wasu kauyuka da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/4SHbJ
Irin makamai da 'yan bindiga ke amfani da shi wajen garkuwa da mutane a NajeriyaHoto: Stefan Heunis/AFP/Getty Images

Wadanda suka shaida lamarin sun ce 'yan kungiyar mai gagwarmaya da makamai sun yi garkuwa da mutanen ne a wasu kauyuka uku na Najeriya da ke kewayen tafkin Tchadi inda suka nemi iyalan mutanen da su biya kudin fansa.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana wa kanfanin dallanci labarun Faransa AFP cewa makiyayan sun hadar da maza da mata, kuma 'yan ta'addan sun ajiye wa iyalansu sako na biyan miliyan 20 na Naira a matsayin kudin fansa.

Tun bayan ballewar kungiyar ISWAP daga cikin Boko Haram, al'ummar kauyukan da ke kewyen tafkin Tchadi ke biyan haraji ga 'yan ta'addan domin gudanar da ayyukansu na noma da kiyo.