1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin Boko Haram ce ta sace daliban makaranta a Kankara?

December 15, 2020

A daidai lokacin da mahukunta a Najeriya ke ci gaba da kokarin kubutar da daliban da 'yan bindiga suka sace a makarantar Kankara da ke jihar Katsina, Boko Haram mai ikirarin jihadi ta dauki alhakin sace yaran.

https://p.dw.com/p/3mkuv
Nigerien Boko Harams Führer Abubakar Shekau
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Sanarwar da shugaban kungiyar ta Boko Haram mai ikirarin jihadi a Najeriya ya fitar a wani sakon murya gami da hotansa mai tsawan mintoci hudu ya dauki alhakin sace daliban. Sakon wanda ya yi a harshen larabci daga bisani ya yi da harshen hausa ya ce "aiki ne da 'yan uwa suka gabatar don daukak addini a kan kafurci, saboda karatun boko ba karatun Allah da Annabi ba ne."

To ko yaya iyayen yaran da aka sace a wannan makaranta suka ji da wannan sanarwa ta Shekau? Ga dai abin da wani mahaifi ke cewa.

Iyayen daliban da aka sace a Kankara, a wani taro da suka yi a harabar makarantar
Iyayen daliban da aka sace a Kankara, a wani taro da suka yi a harabar makarantarHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

"Yarona na daya daga ciki, ajinshi biyu, kuma ni dan cikin garin Kankara ne saboda haka karya yake yi. Wadannan barayin daji ne wadanda aka saba da su da suka dade suna ayyukansu na ta'addanci, tsawon lokaci mai yawa. Amma Shekau karya yake in banda yana neman duniya ta kara jinjina masa, ta kara jin tsoransa. Allah Ya fisu, Ubangiji Allah ya ba gwamnatin nan sa'a da sojoji su karbo mana 'ya'yanmu. Wannan sanarwa ta Shekau yanzu ita ke ta damu hankali a yanzu, da dai ban damu sosai ba, amma tun da na ji wannan sanarwa hankalina ya tashi, sai dai mun dogara ga Allah zai ba mu mafita."

Karin bayani: Najeriya: Dakon mahukunta su ceto daruruwan yara da aka sace a Katsina

Masana tsaro irin su Manjo Bishir Galma mai murabus na da nasu hangen game da ikirarin kungiyar ta Boko Haram kan sace wadannan dalibai.

"Maganar Shekau tuni muna gaya wa mutane cewa fa ko wadanne irin jinsin mutane za su iya fitowa su ce sune suka yi, domin mun sha gani ba a nan Najeriya ba, wurare da yawa da ake irin wadannan fadace-fadacen, sai ka ji an kashe mutanen da suke cewa sune shugabanninsu. A wannan karon ni a ganina wannan karya ne ba wani Shekau da ya je ya turo wadannan mutane ko kuma idan Shekau din ne ma na karya ne, kawai dai sun ce sune don su nuna cewa har yanzu suna da karfi."

Muhammad Abubakar dan shekara 15 da ya kubuta daga hannun 'yan bindigar da suka farma makarantarsu
Muhammad Abubakar dan shekara 15 da ya kubuta daga hannun 'yan bindigar da suka farma makarantarsuHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Sai dai a cewar Barrister Bulama Bukarti mai bincike kan kungiyoyin 'yan ta'adda a nahiyar Afirka na ganin idan ma su Abubakar Shekau suka sace wadannan dalibai, to akwai abin da suka saba yi sai a zura ido a gani.

Karin bayani: Katsina: Zanga-zangar harin 'yan bindiga

"In har ta tabbata su Shekau ne suka yi wannan abin, na tabbata abu na gaba da za su yi shi ne su fitar da faifan bidiyo na wadannan yara su nuna su, don da ma ai suna irin wannan don su samu daukar hankalin duniya. Sannan kuma kila su tattauna da gwamnati domin a ba su kudade a saki wasu daga 'yan uwansu kamar yadda aka yi da yaran Chibok, su kuma sai su sako wadannan yara."

Har kawo yanzu dai mahukunta a Najeriya a matakin gwamnatin tarayya da jihar Katsina ba su ce uffan ba game da ikirarin kungiyar ta Boko Haram kan sace wadannan dalibai. Abin da iyayen yaran suka zura ido dai shi ne mahukunta su ceto masu 'ya'yansu kamar yadda suka yi alkawari.