1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katsina: Zanga-zangar harin 'yan bindiga

Binta Aliyu Zurmi
September 28, 2020

A jihar Katsina da ke tarayyar Najeriya, wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga inda suka toshe hanyar da ta hada Jibiya zuwa cikin birnin Katsina sakamakon yadda 'yan bindiga ke ci gaba da kai masu hare hare. 

https://p.dw.com/p/3j7O0
Nigeria Katsina Sicherheit
Hoto: DW/H. Y. Jibiya

Sama da matasan garuruwa goma ne suka hadu wajen zanga-zangar wadda ta haddasa mutuwar mutum guda wasu kuma suka jikkata kamar yadda wani matashi ya shaidawa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba karin bayani.

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da zanga-zangar a cewar kakakinta SP Isa Gambo, sai dai ya ce suna nan suna kokarin shawo kan masu zanga-zangar kuma nan gaba za suyi cikakken bayani.