Sojojin Najeriya sun kashe Abubakar Shekau | Siyasa | DW | 25.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojojin Najeriya sun kashe Abubakar Shekau

A karon farko rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe mutumin da ke ɗaukar kansa a matsayin jagoran Boko Haram wato Abubakar Shekau.

Rundunar ta sanar da cewar sojojin sun samun gawar mutumin da ke zama jagoran masu tada kayar bayan.Kakakin sojin Najeriyar Manjo Janar Chris Olukolade ya shaida wa manema labarai a birnin Abuja cewar,an kashe Mohammed Bashir yayin fafatawar da aka yi a garin Konduga na Jihar Borno,da ke a yanki arewa maso gabashin ƙasar.
Kuma shi ne yake fitowa a faifan bidiyo a matsayin jagoran ƙungiyar, wato Abubakar Shekau wanda aka daɗe da kashewa.Mun tanadi rahotanni na bita dangane da irin wahalolin da Boko Haran ta janyo wa Najeriya.

DW.COM