Mazauna garuruwan da ke karkashin Boko Haram na cikin matsi | Siyasa | DW | 12.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mazauna garuruwan da ke karkashin Boko Haram na cikin matsi

Duk da cewa akasarin mutanen garuruwan da a halin yanzu ke karkashin ikon 'yan kungiyar Boko Haram sun tsere, amma kuma saura da basu samu tserewa ba, na cikin halin rishin tabbas.

Mutane da ke zaune a cikin garuruwan da ke karkashin ikon 'yan kungiyar Boko Haram da basu samu tserewa ba, na fuskantar yanayi na matsin lamba da rashin sukuni daga masu tada kayar bayan. Kamar dai yadda aka sani, an shafe kwananki da dama da yankunan da ke karamar hukumar Madagali, Michika da ma yankin Bazza, ke karkashin kulawar 'yan kungiyar ta Boko Haram, inda a cikin wata hira da wakilin mu na Yola Abdul-Raheem Hassan, mazauna garuruwa suka ce suna cikin yanayi na tsaka mai wuya da ma hali na rashin tabbas.

Straßenszene in Maiduguri

Mutanen gari na cikin halin rishin tabbas

Halin da wadannan yankuna suka shiga dai, na nuna alamun durkushewar al'amura da dama wanda masana ke ganin zai haifar da koma baya a wadannan garuwa ta fuskoki daban-daban, inda tuni ma wasu suka tabbatar da samun babban koma bayan harkokin kasuwanci.

Ganin irin hali na matsin lamba da mazauna wadannan yankuna ke ciki da 'yan kungiyar ke ikirarin sabon daula a garesu na haddasa ayar tambaya ga makomansu da ta iyalansu, bisa la'akari da yadda suke rasa sukunin gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba sakamakon kwanton da ake yi ana kashe duk wani namiji da suka yi ido hudu da shi, inda da yawa a yanzu sun bar wa Allah hukunci sakamakon gazawa da suke gani daga bangaren jami'an tsaron kasar ta Najeriya.

Sauti da bidiyo akan labarin