Sojojin Najeriya sun kashe Abubakar Shekau | Siyasa | DW | 25.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sojojin Najeriya sun kashe Abubakar Shekau

Kakakin rundunar janar Chris Olukolade ya ce wani Mohammed Bashir da ke ayyana kansa a matsayin Abubakar Shekau ko kuma Abacha Abdullahi Gaidam ko kuma Damask ya rasu bayan wani gwabza faa a garin Konduga.

Kakakin rundunar sojojin asar Janar Chris Olukolade ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja, fadar gwamnatin Tarayyar ta Najeriya, inda ya ce 'yayan Ƙungiyar ta Boko Haram sun miƙa makaman nasu a garuruwan Biu da Mairiga da Buni Yadi da Mubi da kuma Michika bayan mutuwar Shekau. Haka nan ma ya ce wasu sun miƙa makaman ga jami'an tsaro a makoɓciyar Najeriyar wato ƙasar Kamaru.

An daɗe da kashe Abubakar Shekau amma Mohammed Bashir ya ci gaba da yin amfanin da matsayinsa

Olukolade ya kuma tabbatar da cewar sun hallaka wanda ya ke bayyana a faifen bidiyio a matsayin shugaban Ƙungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau mai suna Mohammed Bashir, yayin wata arangama da sojojin suka yi da 'yan ƙungiyar a garin Konduga da ke kimanin kilomita 35 da garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, a tsakanin ranakun 12 zuwa 17 ga wannan wata na Satumba da muke ciki. Dubbun dubatar rayuka ne dai 'yan Ƙungiyar ta Boko Haram suka hallaka a Tarayyar Najeriyar ta hanyar kai hare-haren ta'addanci da bama-bamai da kuma manyan bindigogi.

Sauti da bidiyo akan labarin