Sarkozy ya fara zaman shekaru biyar a gidan yari
October 21, 2025
A wannan Talatar ne tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya soma zaman gidan yari na shekaru biyar bayan da kotu ta same shi da laifin almundahanar kudin yakin neman zabensa da ke da alaka da kudaden tsohon shugaban Libiya marigayi Muammar Gaddafi. Tuni dai 'yan kasar ta Faransa ke ta tsokaci tare da mayar da martani.
Magoya bayan tsohon shugaban mai shekaru 70 sun yi ta rera taken kasar Faransa tare da bayyana sunansa, sa’ilin da yake barin gidansa zuwa gidan yari na La Santé da ke tsakiyar birnin Paris tare da rakiyar matarsa da mawakiya Carla Bruni da ‘ya’yansa da jikokinsa da duk suka halarci taron bankwanan. Nicolas Sarkozy shi ne tsohon shugaban Faransa na farko da zai yi zaman gidan yari tun bayan yakin duniya na biyu.
Kafin shiga kofar gidan yarin, Sarkozy ya fitar da wata sanarwa a shafukan sada zumunta, inda ya bayyana hukuncin da aka yanke masa a matsayin "mummunan cin hanci da rashawa a bangaren shari’a.
Tuni dai lauyoyinsa suka bayyana cewa za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin an saki Sarkozy cikin gaggawa yayin da ake ci gaba da daukaka kara. Wannan lamari ana masa kallon wani babi a kasar Faransa, yana kuma nuna karuwar bincike da hukunta cin hanci da rashawa a matakai na siyasa
A ranar 25 ga watan Satumba ne aka yanke wa tsohon shugaban kasar da ya yi mulki daga shekara ta 2007 zuwa 2012 hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar.
Bayan aka same shi da laifin cewa a lokacin da yake ministan harkokin cikin gida, ya bar wasu makusantansa biyu suka tattaunawa a birnin Tripoli, domin karbar kudaden yakin neman zabensa na shugaban kasa a shekara ta 2007 a asirce daga Muammar Gaddafi na Libya.
Tsohon shugaban mai ra'ayin 'yan mazan mazan jiya, Sarkozy dai ya mulki Faransa daga shekarun 2007 zuwa 2012, yana da shekaru 70, kuma ya zama tsohon shugaban Faransa na farko da aka kai gidan yari tun bayan yakin Duniya na biy