UNICEF ta ce har ila yau ana ci gaba da azabtad da yara a duniya. | Zamantakewa | DW | 06.11.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

UNICEF ta ce har ila yau ana ci gaba da azabtad da yara a duniya.

Hukumar kula da yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF, ta gabatad da sakamakon wani nazarin da ta yi kan azabtad da yara da ake yi a duniya.

Irin yara marayi da hukumar UNICEF ke kula da su a ƙasar Burundi.

Irin yara marayi da hukumar UNICEF ke kula da su a ƙasar Burundi.

Gaba ɗaya dai hukumar ta ce binciken da ta gudanar na nuna cewa, kusan yara dubu 50 ke mutuwa a ko wace shekara a duniya, saboda ɗan karen duka da azabar da ake nuna musu. Sai dai, ba a ƙasashe masu tasowa kawai ne wannan illar ke aukuwa ba. A ƙasashe masu ci gaban masana’antu ma, inda a galibi aka haramta azabtad da yara, rahoton ya ce kusan yara dubu 3 da dari 5 ne ke mutuwa a ko wace shekara saboda azabar da ake nuna musu.

Duk da cewa, sanin kowa ne, azabatad da yara, wata illa ce da ke hana bunƙasar ci gabansu a lokacin da suke tasowa. Kazalika kuma, take hakkinsu ne na ɗan Adam. Amma duk da haka, a ƙasashe da dama na duniya, babu wata doka ko mataki na kare yaran. Kai a wasu wuraren ma, ganin azabtad da yaran ake yi kamar wata kyakkyawar hanya ce ta ladabtad da su da ba su horon kirki. Binciken da Hukumar UNICEF ta gudanar dai na nuna cewa, a kusan ko wace ƙasa ɗaya daga cikin biyu na duniya, an amince ma da dukan yara a makarantu. Bugu da ƙari kuma, fiye da yara miliyan ɗari 2 da 20, maza da mata, masu ƙasa da shekaru 18 da haihuwa ne ake lalata da su, inji sakamakon binciken.

A wata huskar kuma, binciken ya gano cewa, fiye da yara matasa miliyan ɗaya ne ke ɗaure a kurkuku, saboda aikata ƙananan laifuffuka daban-daban, kamarsu sace-sace da dai sauransu. A gidajen yarin ma, ana ci gaba da azabtad fursunoni a ƙasashe da dama, inji ƙungiyar nan ta „End Corporal Punishment“ mai fafutukar yaƙi da gallaza wa fursunoni a duniya, wadda kuma ke aikin haɗin gwiwa da hukumar UNICEF. A ƙasashe 77 na duniya dai, babu wata doka da ke haramta azabtad da furzunoni a jika ta hanyar yi musu duka, da fyaɗe da dai sauransu, inji ƙungiyar. A nahiyar Afirka, ƙungiyar ta ce ƙasashen da ke cikin wannan nau’in sun haɗa ne da Aljeriya, da Botswana, da Ghana, da Mozambik, da Najeriya, da Zimbabwe da Tanzaniya. A nahiyar Asiya kuma ƙasashen da ƙungiyar ta lassafta sun haɗa ne da Afghanistan, da Bangladesh, da Indiya, da Indonesiya, da Iran, da Mongoliya, da Pakistan. Sai kuma a yankin Gabas Ta Tsakiya, inda ƙungiyar ta ce ƙasashen da doka ba ta hana azabtad da fursunoni ba sun haɗa ne da Kuwaiti, da Oman, da Saudiyya. A Latin-Amirka kuma akwai ƙasashe kamarsu Boliviya, da Brazil, da Ecuador, da Guatemala, da Kolombiya, da Mexico da kuma Peru.

Dietrich Garlichs, shugaban reshen hukumar UNICEF ɗin a nan Jamus, ya bayyana cewa:-

„Binciken dai na nuna yadda wannan salon ya yaɗu a duniya, wanda kuma ba shi da wata jibinta da al’adu, ko addini, ko zurfin ilimi. Duk da cewa azabtad da yara na hana ci gabansu matuƙa da kuma take musu hakkokinsu na ɗan Adam, ana gudanad da wannan mummunar ɗabi’ar a yankuna da dama na duiya, inda a wasu ƙasashen ma, ake ganinta kamar wata hanya ce ta ladabtad da su.“

Har ya zuwa yanzu dai, ba a ba da muhimmanci ga yaɗuwar wannan salon azabtad da yara a cikin iyalansu, ko a makarantu, ko gidajen kula da yara, ko gidajen yari ko kuma a wuraren aiki. A yankunan da aka zartad da dokokin haramta salon ma, ba a ɗaukan matakan ganin cewa, an aiwatad da su.

Marta Santos Pais, ta cibiyar binciken Hukumar UNICEF ɗin da ke birnin Florence a ƙasar Italiya, ta tabbatar cewa, har ila yau dai da sauran aiki a gaba wajen shawo kan wannan matsalar:-

„Idan muka dubi halin da ake ciki a duniya a yanzu, za mu ga cewa ƙasashe 14 kawai ne ke da dokokin da ke haramta azabtad da yara a zahiri. Mafi yawansu kuma na nan ne a Turai. Jamus na ɗaya daga cikinsu. Ƙasashe 14 dai, sun yi kaɗan, idan aka yi la’akari da cewa akwai fiye da ƙasashe ɗari 2 a duniyar nan tamu.“

 • Kwanan wata 06.11.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvTB
 • Kwanan wata 06.11.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvTB