UNICEF Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya yana bayar da tallafi kan karatun kananan yara da jinkai musamman a kasashe masu tasowa.
Asusun yana taka rawa wajen ganin bunkasa harkokin ilimi musamman a yankunan karkara. Yana aiki cikin kasashen 190 da ma'aikata wadanda suke kula da yanayin da ake ciki. A shekarar 1946 aka kirkiro asusun.