1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yara fiye da dubu 400 na fuskantar barazanar yunwa

Gazali Abdou Tasawa RGB
April 7, 2023

Yara 'yan kasa da shekaru biyar sama da dubu 400 Unicef ta gano na fuskantar barazanar tamowa a wannan shekara a Nijar.

https://p.dw.com/p/4PpGJ
Yara na fuskantar barazanar kamuwa da cutar tamowa a Nijar
Yara na fuskantar barazanar kamuwa da cutar tamowa a NijarHoto: Million H. Silase/DW

A jamhuriyar Nijar yara 'yan kasa da shekaru biyar sama da dubu 400 na fuskantar barazanar tamowa a wannan shekara a cewar Hukumar Kula da Kananan yara ta Majalisar DInikin Duniya wato Unicef. Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wani rahoto da ta fitar a wannan Jumma'a. Tuni kuma mahukuntan kasar ta Nijar da ma likitoci suka soma tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu.

Rahoton hukumar ta Unicef ya bayyana cewa a jumulce, yara 'yan kasa da shekaru biyar kimanin dubu 970 ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar tamowa sabili da rashin abinci mai gina jiki a kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso a wannan shekara ta 2023, mafi yawancinsu a bisa dalilai na rashin tsaro. 

Matsalar tamowa na kamari a Nijar da Mali da Burkina Faso
Matsalar tamowa na kamari a Nijar da Mali da Burkina FasoHoto: picture-alliance/Photoshot

Unicef ta ce, a Nijar duk da an samu ragewar matsalar idan aka kwatanta da shakarar bara amma matsalar ta fi kamari inda yara sama da dubu 400 ke fuskantar barazanar tamowar a bana. Daga na su bangare, likitoci na gargadin yadda ya kamata mutan karkara masu fama da talauci su iya tunkarar matsalar, dan kare yaransu daga kamuwa da cutar ta tamowa.

Mahukunta da kungiyoyi masu yaki da cutar tamowa a Nijar na cewa, wani abin da ke mayar da hannun agogo baya a wannan kokowa da cutar tamowa shi ne, irin yadda iyayen yara da dama ke sayar da abinci mai gina jiki da aka ba su domin taimaka wa yaransu.