Burkina Faso kasa ce da ke yankin yamma Afirka wadda Faransa ta yi wa mulkin mallaka kafin ta samu 'yanci a shekarar 1960.
Wagadugu ke zama babban birnin kasar kuma kamar galibin kasashen yammacin Afirka ta fuskanci juyin mulki na sojoji, amma harkokin demokaradiyya suna samun inganta a kasar mai matsakaicin arziki.