1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mali: Yajin aiki biyo bayan kama jagoran 'yan kwadago

June 7, 2024

Ma'aikatan bankuna da na gidajen mai gami da na Gidajen inshora sun shigayajin aiki na kwanaki biyu, bayan kama wani babban jigo a kungiyar kwadago bisa zarginsa da yin amfani da takardun jabu.

https://p.dw.com/p/4gnRd
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Sai dai kungiyoyin sun bayyana wannan mataki a matsayin bita da kulli ga duk masu adawa da fadar Bamako gabanin fara wani zaman tattaunawa tsakanin kungiyoyin kwadagon kasar da gwamnati.

A Safiyar Alhamis ranar farko ta fara yajin aikin, al'amuran yau da kullum sun tsaya cik a Bamako babban birnin Mali, lamarin da ke nuna samun karbuwar umurnin dakatar da aiki na sa'o'i 48 da kungiyar ma'aikatan Bankuna da na Gidajen mai gami da na Gidajen inshora ta bayar.

Masu aiko da rahotanni sun ce an samu raguwar zirga-zirgar ababen hawa a Bamakon sakamakon rufe gidajen mai, sannan kuma an samu karancin hada-hada a kasuwanni da shaguna saboda bankunan kasar sama da 15 sun kasance a kulle.

Fushin ma'aikatan da ya jefa 'yan Mali cikin garari a daidai lokacin da ake shirye-shiryen babbar Sallah, martani ne ga matakin gwamnatin mulkin sojin kasar na tsare mataimakin sakataren uwar kungiyar kwadago ta kasa UNTM Hamadoun Bah a gidan yari kan tuhumarsa da yin amfani da takardu na jabu a takkadamar cikin gida da ta taso a cikin kungiyarsa.

An dai izar keyar dan gwagwarmayar gidan yari ne a jajibirin wata ganawa da jagoran gwamnatin mulkin soja Kanal Assimi Goita ya yi da kungiyoyin kwadagon kasar, lamarin ya sa ake siffantawa matakin da tauna tsakuwa don aya ta ji tsaro a daidai lokacin da adawa ta fara fitowa fili ga matakin fadar mulki ta Bamako kan yunkurinta na neman dawoma kan madafun iko.

To amma Sidi wani mazaunin Bamako da yajin aiki ya shafi harkokinsa ya ce hukumomin mulkin sojan Malisu iya kaucewa wannan yanayi da aka fada domin abune da ka iya daudada tasirinsu a idon 'yan kasar.

'' Hakika al'amari ne mai matukar wahala da 'yan Mali suka shiga a wannan lokaci. Kwanaki 10 suka rage kacal a gudanar da bikin sallar Layya kuma bai dace a daidai wannan lokaci a shiga cikin irin wannan yanayi ba. A bayyane take dole ne mahukunta su yi taka tsan-tsan da irin abubuwan da ka je su dawo idan za su dauki wasu matakai. Sun san sarai cewa za iya shiga damuwa idan suka kama wannan dan gwagwarmaya.''

Wannan jajin aiki da ba a taba ganin irinsa ba a nan da shekaru hudu tun bayan zuwan sojojin kan madafun iko ya girgiza Mali matuka lamarin da ya sa wasu 'yan kasar ke fadar ba dadi. To amma Alasan wani da ya je banki neman kudin  amma ya tarar da kofofinsu na rufe, cikin bacin rai ya ce idan har kungiyoyin kwadago sun yi imanin ba bu wanda ya fi karfin doka, a maimakon tsinduma yajin aiki kamata ya yi su jira sakamakon shari'a domin gaskiya za ta yi halinta.

''Na yi imanin cewa alkalai na da cikakkar dama ta yi wa ko wani dan kasa shari'a. Sannan kuma ina da yekinin cewa gurfana a gaban kotu ba ya nufin samun mutum da laifi.  Amma gaskiyar lamarin yajin aikin nan na bankuna yajefamu cikin mugun yanayi la'akari da halin yaki da Mali ke ciki baya ga fatara da talauci da suka yi wa jama'a katutu. Sannan kuma hujjojin da kungiyar ma'aikatan ta gabatar domin shiga wannan yajin aiki ba su gamsar ba.'' 

Har kawo yanzu dai uwar kungiyar ma'aikatan Mali ta UNTM ba ta ce uffan ba a game da wannan batu da ta ce tana bibiya a tsanake, amma takwararta ta SYNABEF ta yi gargadin tsindumi yajin aikin sai baba ta gani daga Litinin mai zuwa muddin ba a samu masalaha ba, yayin da su kuwa kungiyoyin aikalai suka bukaci mambobinsu da su nisanta kansu daga wannan sabuwar turka-turka.

To amma a yanzu haka dai gwamnatin Mali ta fara tattaunawa da kungiyoyin domin samar da mafita kan wannan yajin aiki da ya dabaibaye muhimmam fannonin rayuwa.