1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

EU za ta rufe sansaninta na horon sojoji a kasar Mali

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 9, 2024

Tun a shekarar 2022 EU ta dakatar da ayyukanta a Mali, bayan da sojojin da ke mulki a kasar suka ayyana ficewa daga kungiyar kasashen G5 Sahel

https://p.dw.com/p/4ff4B
Hoto: Thomas Wiegold/photothek/picture alliance

Kungiyar tarayyar Turai EU ta ce za ta rufe sansaninta na horon sojoji a kasar Mali da zarar wa'adin da take aiki da shi na 18 ga wannan wata na Mayu ya cika, bayan shafe shekaru 11 tana bai wa sojojin Mali da na kasashen G5 Sahel horon yaki da ta'addanci.

Karin bayani:Jamus ta kammala kwashe sojojinta daga Mali

Tun a shekarar 2022 EU ta dakatar da ayyukanta a Mali, bayan da sojojin da ke mulki a kasar suka ayyana ficewa daga kungiyar kasashen G5 Sahel.

Karin bayani:MINUSMA ta kawo karshen aikinta a Mali

Mali dai ta fada hannun sojoji ne tun cikin shekarar 2020, yayin da sojojin da ke mulki yanzu suka kwace iko a cikin shekarar 2021, sannan suka alkawarta mika mulki ga gwamnatin dimukuradiyya bayan wa'adin shekaru 2, amma a cikin watan Satumban bara suka sanar da jingine wannan alkawari na zaben Fabarairun bana.

'Dage zaben dai ya janyo cece-ku-ce da kuma martani mai zafi daga bangaren 'yan siyasar kasar.