Eurozone kungiya ce ta wasu kasashen da ke nahiyar Turai da ke amfanin da kudin nan na bai daya na Euro. Wannan kungiya dai na da kasashe 19 da ke karkashinta.
Jamus da Farasa na daga cikin manyan kasashen da ke karkashin kungiyar Eurozone. Kasashse irinsu Austiriya da Beljiyam da Cyprus da Estoniya da kuma Finland na karkashin wannan kungiya. Sauran sun hada da Girka da Italiya da Latviya da Lithuaniya da Luxemburg da Malta da Holland da Portugal da Silovakiya da Siloveniya da Spaniya. Yawan mutanen da ke wadanannan kasashe suka kunsa da sun haura miliyan 300.