1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jinkiri har yanzu wajen fitar da kudin Eco

Abdoulaye Mamane Amadou AH
July 8, 2024

Har yanzu akwai cikas game da batun samar da kudaden bai daya da kasashen da ke yankin yammacin Afirka suka kudiri aniyar kashewa a tsakaninsu shekaru aru-aru da suka gabata.

https://p.dw.com/p/4i1bs
Hoto: K. Schmitt/Fotostand/picture alliance

 Sai dai kalubalen da kasashen yankin renon Faransa suke fuskanta da ya sha banban da na masu amfani da harshen Ingilishi na kara saka dan ba kan makomar kudin duk da muhimmancinsu ga tattalin arzikin yankin na yammacin Afirka. Abdoulaye Mamane Amadou ya duba mana wannan batu ga kuma rahotonsa. Shekaru fiye da 20 kenan da kasashen yankin yammacin Afirka suka bijiro da manufarsu ta kafa kudin bai daya, manufar kasashen ita ce ta saukaka huldar kasuwanci da habaka tattalin arziki, baya ga batun yaukaka shige da fice da suka fara mora a karkashin kungiyar   ECOWAS.

Kokarin bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen yankin 

Symbolbild | Geld Währung Euro
Hoto: Wolfilser/Zoonar/picture alliance

Amfani da kudin zai kawo karshen nau'ukukan kudade bakwai da ke zagayen kasashe 15 na yankin, kana tare da samar da tattalin arziki madaidai ci da zai ba wa kasashen damar tunkarar abokanin hulda daga ko ina na sassan duniya. Sai dai kuma tsarin da ya kamata a ce ya soma aiki a shekarar 2020 na ci gaba da samun tazgaro, walau daga manyan kasashen yankin mafi karfin tattalin arzikiirinsu tarayyar Najeriya da ke amfani da kudin Naira, har izuwa ga na renon Faransa da masana ke cewa Shugaba Ouatara da kasancewa dan koren CFA. Dr Shu'aibu Idriss Mikati masanin tattalin arzikin kasa da kasa ne ya ce akwai wasu abubuwan na daban da ke faruwa masu muhimmanci da ke hana ruwa gudu ga wannan  manufa.

Faduwar darajar kudaden kasashen yankin na yammacin AfirkaTattalin arzikin yankin dai na kara fuskantar matsin lamba, ga misali a Najeriya, Naira ta shiga gararin koma bayan da ba ta taba fuskanta ba a tarihi, takardar kudin Ghana na Sidi na cikin tsaka mai wuya, hasali ma in baya ga kudin Francs CFA ba wasu kudin a yankin yammacin Afirka da ke da wani tabbas. Sai dai a cewar Malam Ibrahim Adamou Louche masanin tattalin arziki da ke bibiyar batun na samar da kudin Eco mai zama a Faransa, da akwai wasu karin kalubalen da ke addabar sabon shirin wanda ya zarta wanda ya kunno kai a yayin mullin Shugaba Buhari da ya yi kememen cewa tsarin ba zai ba wa kasarsa kariyar tattalin arzikin da take bukata ba, hasali ma Faransa na son cin  moriya.

Europäische Währung | 100 Euro-Scheine werden gedruckt
Hoto: DesignIt/Zoonar/picture alliance