Kungyiar Tarayyar Turai kungiya ce da ta hada kasashen Turai kimanin 28 wadda aka kafa ta don ci gaban tattalin arziki da harkokin siyasa.
Beljiyam da Faransa da Jamus da Luxemburg da Holland suka bijoro da kungiyar ta EU a shekarar 1957 bayan da suka sanya hannu kan wata yarjejeniya da suka yi a birnin Rome na Italiya. A birnin Maastricht na Holland ne aka karkare batun kafa EU a shekara ta 1993.