1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD na fargabar fantsamar rikicin kasashen Sahel a makwabta

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 30, 2024

Rikicin ya fara shafar kasashen Guinea da Togo Jamhuriyar Benin da Ghana da kuma Cote d'Ivore, har ma da Mauritania da kuma Algeria

https://p.dw.com/p/4gSX9
Hoto: Marco Simoncelli/DW

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce matukar aka gaza daukar matakan agajin gaggawa wajen warware rikice-rikicen da suka addabi yankin kasashen Sahel, to hakika tashin hankalin zai fantsama zuwa wasu kasashe makwabta, tare da zama karfen kafa ga duniya.

Karin bayani:Yaduwar rikicin Sudan a yankin Sahel

Babban jami'in hukumar mai kula da yammaci da kuma tsakiyar Afirka Abdouraouf Gnon-Konde, ya shaidawa manema labarai a birnin Brussels cewa zaman dar-dar da ake fama da shi a kasashe irin su Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, sakamakon hare-haren ta'addanci, na zama barazana ga kasashe makwabta.

Karin bayani:ECOWAS: Sake tattaunawa da sojojin Nijar

Ya kara da cewa tuni rikicin ya fara shafar kasashen Guinea da Togo Jamhuriyar Benin da Ghana da kuma Cote d'Ivore, har ma da Mauritania da kuma Algeria.

Hukumar kula da kasashen Turai ta alkawarta bayar da tallafin Euro miliyan 201, kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 218 ga mabukata, a kasashen Burkina Faso da Kamaru da Chadi, sai Mali da Mauritania da Jamhuriyar Nijar da kuma Najeriya.