1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Warware rikicin Nijar ta diflomasiyya

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 19, 2023

A kokarin da take na tabbatar da ganin ta dauki matakin diflomasiyya a kan sojojin da suka kifar da gwamnati a Jamhuriyar Nijar, kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta isa Yamai da nufin sake tattaunawa da su.

https://p.dw.com/p/4VMMF
	
Nijar | Yamai | Abdourahamane Tiani
Jagoran gwamnatin juyin mulkin soja ta Nijar Abdourahamane TianiHoto: Télé Sahel/AFP

Wakilan kungiyar ta Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO karkashin jagorancin shugabanta da kuma ke zaman shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ta ia Yamai, inda suke shirin tattaunawa domin lalubo hanyar warware rikicin tare da tallafin wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Afirka ta Yamma da Sahel Leonardo Santos Simao da ya isa tun a ranar Jumma'ar da ta gabata. Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce Simao zai gana da jagoran juyin mulkin da kuma sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da gaggaita shawo kan rikicin da Nijar din ke ciki.