1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNa duniya

Matsalar tarbiyya a tsakanin matasa 'yan mata a yankin Sahel

Gazali Abdou Tasawa
May 15, 2024

Nazari kan matsalar lalacewar tarbiyar matasa a kasashen yankin Sahel tare da shawarwarin yadda kungiyoyi da mahukunta za su hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalar da ke yin illa ga zamantakewar al'ummomi.

https://p.dw.com/p/4ftf2
Mata a Jamhuriyar Nijar
Mata a Jamhuriyar NijarHoto: piemags/IMAGO

Shigowar sabbin dabi'u kamar madigo da luwadi da shaye-shaye a tsakanin matasa musamman 'yan mata na yin barazana ga makomar tarbiyyar matasa a kasashen yankin Sahel da suka hada da Nijar da Mali da Burkina Faso. 

Matan na kasashen kungiyar AES sun nuna damuwa kan yadda suka ce wasu kungiyoyin kasa da kasa masu taimaka wa kasashen nasu ke fakewa da wasu tsare-tsare da suke gabatarwa wajen shigo da miyagun dabi'u a tsakanin matasa da kuma yadda a cikin gida iyaye ke nuna sakaci wajen tarbiyar da 'ya'yansu.

Sai dai taron matan kasashen na AES ya bayar da shawarwari kan irin mu'amalar da iyaye ya kamata su yi da 'ya'yansu wadanda za su taimaka ga kyautata tarbiyar matasan maza da mata. 

Taron ya fitar da jerin shawarwari na yaki da gurbatar tarbiyar matasa da kuma na inganta ta, shawarwarin da kungiyoyin matan za su gabatar ga mahukuntan kasashen na AES.