Sudan ta ki amincewa da kudirin tura sojin Majalisar dinkin duniya | Siyasa | DW | 24.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sudan ta ki amincewa da kudirin tura sojin Majalisar dinkin duniya

Babbar Jamíyar National Congress dake mulki a Sudan ta ce ba zata sabu ba, tura sojin Majalisar dinkin duniya zuwa Dafur

Halin rayuwar yan Gudun hijira a Dafur

Halin rayuwar yan Gudun hijira a Dafur

Jamíyar wadda ta yi kakkausar suka ga daftarin kudirin ta kuma yi kashedi mai tsaúri ga ƙasashen Amurka da Britaniya waɗanda suka jagoranci gabatar da daftarin ga Majalisar ɗinkin duniya. A cewar shugaban Jamíyar ta National Congress mai mulkin ƙasar Sudan, Ghazi Salah Eldin Atabani daftarin ƙudirin shi ne mafi muni kuma mafi haɗari fiye da sauran matakai da aka sanyawa ƙasar a baya, domin a cewar sa, maƙasudin wannan ƙudirin shi ne yiwa ƙasar tarnaki da dabai bayi ta kowace fuska. Yace ko kusa ba zata saɓu ba domin kuwa ba zasu amince da ƙudirin ba komai rintsi. Ghazi Sala Eldin ya ƙara da cewa dukkan ƙasar da ta gabatar da ƙudirin bata buƙatar alhairi ga ƙasar Sudan.

A makon da ya gabata, Amurka da Britaniya suka gabatar da daftarin ƙudirin ga kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin dinkin duniya duk kuwa da kurari da barazanar da gwamnatin sudan ta yi na farma dakarun da suka kuskura suka sanya ƙafar su a yankin. Dakarun da ake shirin turawa ƙarkashin jagorancin Majalisar ɗinkin duniya za su maye gurbin sojojin kiyaye zaman lafiya ne na ƙungiyar haɗin kan Afrika wadda ke fama da ƙarancin kayan aiki da kuma suka kasa dakatar da kashe kashe da fyaɗe da kuma rigingimu dake sanya fararen hula yin ƙaura daga wannan gari zuwa wancan.

A ranar Litinin mai zuwa kwamitin sulhun na Majalisar ɗinkin duniya zai gudanar da taro domin tattauna matsanancin halin da ake ciki a yankin na Dafur. Muƙaddashin sakataren Majalisar ɗinkin duniyar Mark Malloch Brown ya baiyana halin da ake ciki a Dafur din da cewa abin takaici ne matuka. Shi kuwa wakilin ƙasar Ghana kuma shugaban kwamitin tsaron na Majalisar ɗinkin duniya Nana Effah Apenteng ya buƙaci samun masalaha kafin tura sojojin na gamaiyar ƙasa da ƙasa. Yace akwai buƙatar samun haɗin kai da goyon bayan gwamnatin Sudan kafin a iya aiwatar da ƙudirin tura sojojin cikin nasara.

A cigaba da rikicin dake faruwa a Dafur ɗin, wasu sojoji biyu na ƙasar Rwanda dake cikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta ƙungiyar gamaiyar Afrika sun rasa rayukan su, a wani harin kwantar bauna da wasu yan bindiga daɗi suka yi musu, abin da kuma ke ƙara ƙarfafa kiran da Amurka ke yi na tura runduna mai karfi ta Majalisar ɗinkin duniya domin maye gurbin sojojin na ƙungiyar Afrika wajen kula da shaánin tsaro da kuma kare zaman lafiya a yankin. Kakakin maáikatar harkokin wajen Amurka Gonzalo Gallegos yace irin wannan tarzoma yana nuni da yadda tabarɓarewar tsaro take a Dafur wanda a sakamakon sa, a kulli-yaumin ake kashe fararen hula da maáikatan agaji waɗanda basu ji ba basu gani ba, wanda kuma ke haifar da tsaiko wajen kaiwa alúmar Dafur ɗin taimakon jin kai.

Sudan wadda ta ki bada kai ga buƙatar, a farkon wannan watan ta mikawa Majalisar ɗinkin duniya nata tsarin wanda ya ƙunshi tura sojin ƙasar domin aikin kiyaye zaman lafiyar maimakon dakarun Majalisar ɗinkin duniya. Shugaban ƙasar Sudan Omar al-Bashir ya yi gargaɗi da cewa yankin na Dafur wanda ke dabaibaye da rikici yau kusan shekaru uku da rabi zai zama maƙabarta ga sojojin na yammacin turai. Al Bashir ya ƙara da cewa Amurka da ƙasashen yammacin turai na kitsa wani makirci ne na yiwa ƙasar mulkin danniya. Yana mai cewa abin da ke faruwa a yanzu haka a Lebanon shi ne kwatankwacin abubuwan da suka faru a ƙasashen Palasdinu da Afghanistan da kuma Iraqi, kuma shi ne abin da ake neman haifarwa a Dafur da kuma gabashin Sudan.